Gwamnatin Najeriya ta yi wa ?ungiyar malaman jami’o’i na kasa bayani kan dalilan da suka sa aka samu jinkiri a biyan ku?aden da ta yi alkawarin bayarwa bayan yarjejeniyar da suka cimma a baya.
Ministan Ilimi, Emeka Nwajiuba, ya shaida wa jaridar The Punch cewa gwamnati na aiki tukuru domin tabbatar da cewa an saki ku?a?en da aka yi musu alkawari daga babban bankin kasa wato CBN.
Sai dai ASUU, a martaninta ta yi watsi da hujjojin ministan, tana mai cewa gwamnati na nuna rashin gaskiya da yaudara kan jinkiri da ake gani na biyansu hakokinsu.
A ranar Litinin dai ASUU ta yi barazanar sake tsunduma yajin aiki muddin aka gagara biya mata bukatunta.
A 2020, malaman jami’o’in suka gudanar da yajin aikin wata 9 abin da ya kai ga durkusar da harkar ilimi a kasar.
Daga bisa malaman sun amince su koma bakin aiki bayan cimma wasu yarjeniyoyi da suke cewa har yanzu ba a cika ba.Article share tools
