An kirayi al umma musulmai musammanma matasa da suyi dukkanin abin da ya dace domin hadin kan al umma su kuma nisanta kansu da duk abida zai kawo tashin hankali a tsakanin jama a baki daya.
Shuwagabannin kungiyoyin matasa musulmai dana kirista ne sukayi wannan kira a taron manema labarai a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Rev Gabriel L Shall shine shugaban kungiyar matasa kiristoci a jahar Adamawa yace kiran ya zama wajibi duba da irin abunda yake faruwa a fadin kasanan na rashi jutuwa da ake samu a tsakanin musulmai da kiristoci wanda kuma hakan ba dai dai bane.
Don haka ya kamata mabiya addini musulunci dana kirista su kasance masu kwanar junansu a koda yaushe tare kuma da hada Kansu wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen samar da zaman lafiya a fadin Najeriya baki daya.
Ya kuma sanar da cewa matasa musulmai dana kirista a jahar Adamawa kansu a hade yake don hakanema ya kirayi matasan da su nisanta kansu da wanda ke amfani dasu wajen tada hankalin jama a.
Harwayau ya kirayi gwamnatin data kara himma wajen samarwa matasa aikinyi wanda hakan zai taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a fadin kasan baki daya.
Rev. Gabriel ya koka da yadda aka raba kasuwanci a tsakanin musulmai da kiristoci a jahar Filatau wanda kuma hakan ban daceba kasancewa ana zaune kasa daya al umma daya.
Shima anashi jawabi ahugaban kungiya matasa musulmai a jahar Adamawa Abdullahi ibn Hamman kiran matasan ya yi da cewa suyiwa kansu kiyamun laili su nisanta kansu daga duk abinda zai bata musu rayuwarsu dama zubar musu da mutuncin a idon al umma.
Shima ya shawarci gwamnati da ta yi dukkanin maiyiwa domin ganin an fidda matasan daga cikin kangin rashin aikinyi domin magance saman bŕnza a tsakanin matasan baki daya.
Abdullahi ya kuma kirayi iyaye da suma auna da rawanda zasu iya takawa wajen hada kan matasan ta wajen basu tarbiya da ta dace.
Sun kuma yi Allah wadai da abinda ya faru a jos na kisan matafiya wadanda basujiba ba su ganiba wanda kuma wannan abun takaicine kuma ya kamata a hukunta duk wadanda aka samu da hanu acikin wannan aika aika.
Sun kuma kirayi yan Najeriya da su cigaba dayin adu o i a kada yaushe domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo dukkanin kalu balen tsaro dakeciwa gwamnati dama al umman kasan nan tuwo a kwarya.
