Tabarbarewar Tsaro: Najeriya Na Bukatar Addu’a – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam JNI Sa’ad Abubakar, ya bukaci al’ummar Musulmi da su yi addu’a ta musamman domin Allah ya kawo karshen kalubalen da Najeriya ke fuskanta.

Wannan kiran na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren JNI Dakta Khalid Aliyu ya fitar ranar Alhamis a Kaduna.

Mai alfarma Salam Abubakar ya kuma bukaci alhazan Najeriya da ke Saudiyya da su yi wa Najeriya da shugabanninta addu’a a ranar Arafat.

Related posts

Leave a Comment