Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban kungiyar Jamaatu Nasril Islam JNI Saad Abubakar, ya bukaci alummar Musulmi da su yi addua ta musamman domin Allah ya kawo karshen kalubalen da Najeriya ke fuskanta.
Wannan kiran na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren JNI Dakta Khalid Aliyu ya fitar ranar Alhamis a Kaduna.
Mai alfarma Salam Abubakar ya kuma bukaci alhazan Najeriya da ke Saudiyya da su yi wa Najeriya da shugabanninta addua a ranar Arafat.

