An Damke Matashin Da Ya Yi Wa Maryam Booth Kazafi

Rahoton dake shigo mana daga masana’antar Kannywood na bayyana cewar Shahararriyar jaruma Maryam Booth, ta sa an cafke mata wani matashi da ta zarga da yada labarai na karya kan ta inda aka sa shi yin bidiyo domin neman afuwar ta da janye miyagun kalamansa.

A kwanakin baya, labarin cewa Maryam Booth ta koka da yadda ba a saka ta fina-finai tun bayan bayyana bidiyon tsiraicin ta ya bazu.

Kamar yadda kagaggen labarin ya bayyana, jarumar ta shiga damuwa kuma ta ce ta na neman miji ido rufe domin ta yi aure ta huta. Babu shakka labarin ya karade kafafen sada zumuntar zamani inda kowa ke fadin albarkacin bakinsa da maganganu marasa dadi a kan jarumar.

A cikin makon nan kuwa jarumar ta wallafa wani dogon rubuta na jan kunne da kakkausar murya tare da bidiyon wani matashi da ta bayyana cewa shi ya yada labarin karya a kan ta.

Ta ce daga yanzu duk wanda ya yi mata irin wannan karairayin, ko mahaifiyar da dan uwan ta, to babu shakka za ta dauka mataki a kai. Kamar yadda ta wallafa a shafin ta na Instagram:

“Kwanaki wata jita-jita ta dinga yawo a kan cewa na tattauna da yaron nan ina neman mijin aure na rasa da sauran miyagun abubuwa dangane da ni. “Toh duk karya ce kuma wannan yaron ne ya shirya. Zan so in ja kunnen wadannan bata-garin ‘yan jaridan balle wadanda ke yanar gizo ballantana na YouTube.

“Daga yanzu zan dauka matakin shari’a kan duk wata kafa da ta wallafa labari a kaina ko ‘yan uwana ba tare da tabbatarwa daga wuri na ba. “Ba zan iya jure ganin mutanen da suka mayar da hankali wurin bata mana suna ba ballantana marigayiyar mahaifiyata.

Daga karshe bayan an kama mutum sai ka ji ana cewa “ka yi hakuri ka fi karfin hakan”. “Amma ba za su tuna hakan ba lokacin da suke mugun abu. Na yadda shuhura ta na zuwa da abubuwa da yawa, sai dai kuma barna ma haka. Nagode.”

Amma kuma a bidiyon da jarumar ta wallafa na yaron, ya ce shafin Rariya ne suka wallafa labarin, shi kuwa ya yi tsokaci mara dadi a kasan labarin amma ya na neman afuwarta.

Related posts

Leave a Comment