Babban hafsan hafsoshin Najeriya Manjo Janar Christopher Musa da babban hafsan sojin ?asar na ?asar Manjo Janar Toareed Lagbaja sun yaba wa dakarun sojin ?asar musamman wa?anda ke fagen daga, bisa sadaukarwa da kishin ?asa da jajircewa da suke nunawa wajen tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ha?in kan ?asar.
“Tabbatar da tsaro da ci gaban ?asarmu wani babban nauyi ne da ya rataya a wuyan kowanne ?an Najeriya”, kamar yadda dakartan ya?a labaran hukumar tsaron ?asar ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin babban hafsan tsaron ?asar.
Janar Musa ya tabbatar wa jami’an tsaron ?asar irin goyon bayan da yake ba su a ?o?arinsu na gudanar da ayyukansu.
A nasa ?angare, babban hafsan sojin ?asa na ?asar Manjo Janar Toareed Lagbaja ya yaba wa sojojin ?asa na Najeriyar dangane da saudaukarwa da jajircewa da ya ce sojojin na nunawa wajen gudanar da ayyukansu a fa?in kasar.
Ya kuma yi kira ga dakarun sojin su ci gaba da nuna jarunta da kishin ?asa a yayin gudanar da ayyukansu.
A makonni biyu da suka gabata ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya na?a sabbin hafsoshin tsaron ?asar, bayan sauke tsoffin dakarun tsaron.
