Shugaban kasa Bola Tinubu wanda ya yi sallar Idi a birnin Lagos ya amince cewa Najeriya na fuskantar kalubale mai tarin yawa amma kuma a cewarsa yana kokarin samar da hanyoyin magance matsalolin.
A cikin sanarwar da ya fitar na taya musulmin Najeriya murnar Barka da Sallah, Asiwaju Tinubu ya ce “Dole ne mu gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya ba mu damar halartar wata Sallar Idi”.
Ya ?ara da cewa Allah ba ya ?ora wa mutum abin da ba zai iya ?auka ba.”
“Allah Ya san halin da ?an Najeriya ke ciki kuma zai kawo musu sau?i.”
Sannan ya bu?aci al’umma da su yarda cewa ?asar za ta gyara, su kuma ha?a hannu wajen cimma nasarar hakan.
Ya kara da cewa gwamnatinsa ta fara neman hanyar magance matsalolin da ke addabar kasar ta hanyar shawarwarin da suke samu daga wajen kwararru don gyara tattalin arzi?i da kuma kawarda duk wani cikas da zai hana bun?asar Najeriya.
