Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin na zamani Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana irin ?alubalen da ya fuskanta a lokacin da ya ke minista. Pantami ya zayyano wasu abubuwa guda hu?u da ya ce muddun kana da ?aya daga cikinsu, za ka fuskanci ?alubale mai yawa.
Ya yi bayanin ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Sunna TV a birnin Makkah na ?asar Saudiyya a ?arshen makon da ya gabata.
Pantami ya ce duk wata nasara da ya samu a lokacin da yake ofis, ya sameta ne daga wurin Allah ma?aukakin sarki, inda ya ce tun da ya fara aiki, bai yi watsi da addu’a ba.
Ya ce baya gajiwa wajen yin addu’a a koda yaushe, haka nan ma yakan fa?awa ‘yan uwa da abokan arzi?i cewa su taya shi da addu’a akan Allah ya ba shi ikon sauke nauyin da aka ?ora masa.
Pantami ya ce ba dole ba ne a samu wani daga cikin musulmai, da ya fuskanci irin ?alubalen da ya fuskanta a yayin gudanar da ayyukansa. Ya ?ara da cewa akwai wasu siffofi guda uku da in kana da ?aya daga cikinsu, zaka fuskanci bin diddi?i, yarfe, da ?azafi musamman daga wasu daga jaridun kudancin Najeriya.
