Peter Obi: Fulani Sun Yi Wa Miyyeti Allah Tawaye

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa wata kungiyar kwararrun Fulani, Coalition of Fulbe Professionals in Africa (COFPIA), a ranar Litinin, 15 ga watan Agusta ta nisanta kanta daga wata sanarwa da Miyetti Allah Kautal Hure ta yi na kiran kar a za?i ?an takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Peter Obi.

A baya dai kungiyar Miyetti Allah ta ce al’ummar Fulani ba za su goyi bayan takarar Peter Obi ba, inda ta bayyana shi a matsayin mutum mai tsananin kabilanci.

Kungiyar ?wararrun Fulanin ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da duk wani furucin da kungiyar Miyetti Allah ta yi tare da cewa Miyetti Allah ba ta magana da muryar kabilar Fulani bane.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta na kasa Farfesa Mohammed Gidado da sakatariyarsa Hajiya Mairo Modibo ta ce: “Kungiyar Fulani a duk fadin Najeriya ba za ta makance da wannan maganar ta Miyetti Allah ta siyasa ba. “Fulani a yanzu sun waye kuma ba za a yi amfani da su a matsayin kayan yada ra’ayin addini ba.

Za mu wayar da kan jama’armu don kada kuri’ar cancanta da kwarewa a 2023. “Ba za mu taba zabar duk wani dan takara da ba shi da wani abin da zai iya ba, mun wuce batun ra’ayin addini da kabilanci. “Za mu zabi shugaban da zai magance talauci da matsananciyar yunwar da ta dami mutanenmu na tsawon lokaci.

Related posts

Leave a Comment