Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa yana daya daga cikin mutane 37 da suka daura tsintsiyar jam’iyyar APC tun farko don haka ya dauki jam’iyyar a matsayin daya daga cikin ‘ya’yansa, wanda babu ranar rabuwa.
Gwamnan wanda ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta kai tsaye a gidajen rediyon Kaduna a daren Laraba, ya karyata jita-jitar da ake yadawa na cewa yana shirin sauya sheka zuwa wata jam’iyya, kan batun Tinubu da Shettima.
El-Rufai ya sha alwashin ci gaba da kasancewa a jam’iyyar APC har zuwa karshen rayuwarsa, inda ya kara da cewa ‘’idan na bar APC, to na bar siyasa gaba daya’’.
Dangane da batun cire tutar APC da ke kan motarsa, gwamnan ya yi karin haske da cewa, ka’ida ne da zarar karfe shida na yamma ta yi, kowace tuta ko dai a sauke ta idan tana kafe a kan sanda, ko kuma a rufe ta idan tana kan abin hawa ne.
Gwamnan ya ce wannan ba shi ne karon farko da masu yada jita-jita ke kulla masa makirci ba, inda ya ce: ”Sun ce ina son zama shugaban kasa, sai suka zo suka ce ina so in zama mataimaki a takara, a yanzu kuma sun ce DG kamfen.”
El-Rufai ya kuma nanata cewa, Muhammad Sani Abdullahi, tsohon kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi, har yanzu shi ne dan takarar jam’iyyar APC na mazabar Kaduna ta tsakiya, inda ya karyata rade-radin da ake yadawa na cewa ya yi shirin korarsa.
