Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Ministan Sufuri Injiniya Mua’zu Jaji Sambo ya ce babu ranar da za a koma da sufurin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna har sai an sako dukkanin fasinjojin da aka sace tare da samar da karin matakan tsaro.
Ministan ya bayyana hakan ne bayan da ya kai ziyarar duba tashar jirgin kasa da ke Idu a Abuja ranar Talata.
An ruwaito cewa Ministan ya bayyana cewa za a samar da na’urar tsaro ta musamman da za ta rinka sanya ido kan titin jirgin.
A baya dai Majalisar zartarwa ta yi watsi da bukatar da tsohon ministan sufuri ya gabatar ta samar da kudin sayen wannan nau’ra Naira miliyan dubu uku.
Ministan ya ce, abu ne mai matukar muhimmanci a tabbatar da an ceto ‘yan kasar da aka sace sun koma ga iyalansu, idan ba haka ba za a ga kamar gwamnati ba ta damu ba, alhalin kuma gwamnatin na yin duk abin da za ta iya yi domin ta ga an sako su sun sake haduwa da iyalansu.
