Kashin Shettima, Za?a??en Mataimakin Shugaban ?asa, ya bayyana dalilin da ya sa APC, Tinubu da shi kan sa su ka yanke shawarar amincewa Godswill Akpabio ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.
Ya ce Za?a??en Shugaban ?asa, Bola Tinubu ne ya yi zurfin tunani da hangen nesa cewa kada Musulmi ya yi Shugaban Majalisar Dattawa.
Da ya ke wa Tajuddeen Abbas da tawagar sa bayani yayin da su ka kai masa ziyara a ranar Juma’a, Shettima ya ce sun fahimci bai kamata a ce Shugaba da Mataimaki da Kakakin Majalisa duk Musulmi ba ne, sannan kuma a ce Shugaban Majalisar Dattawa shi ma Musulmi ne ba.
Haka kuma ya ce Tinubu ba zai tafka irin kurakuren da Jonathan da Buhari su ka tafka ba – Shettima
Za?a??en Mataimakin Shugaban ?asa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu za ta kauce daga maimaita irin kurakuren da gwamnatocin Jonathan da Buhari su ka tafka wajen za?en shugabannin Majalisar Tarayya.
Shettima ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, inda ya tunatar da rikicin da ya haddasa Mambobin Majalisar Tarayya su ka za?i wanda ba shi jam’iyya ke so ba.
Ya ce tsohon Shugaban ?asa Goodluck Jonathan ya yi sakacin kasa iya ri?e ragamar mulkin sa tun a ranar Aminu Tambuwal ya zama Kakakin Majalisar Tarayya. Ya ?ara da cewa wannan lamari ne ya ?ara zama dalilin fa?uwar PDP a za?en 2015.
Shettima ya ce shi kuma Shugaba Mai Barin Gado, Muhammadu Buhari, ya kasa samun gagarimar nasara a shekaru hu?un sa na farko, saboda an za?i shugabannin majalisa wa?anda ba su ne jam’iyyar APC ke so ba.
Shettima ya bayyana haka yayin ganawar sa da Tajuddeen Abbas da Ben Kalu, wa?anda su ne APC da Tinubu ke so su zama Kakakin Majalisa da Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya.
An yi ganawar tare da gungu ko gamayyar mambobi masu biyayya ga za?in da jam’iyya ta bayar a batun shugabancin Majalisa.
Tuni dai mambobin da ba su goyon bayan Abbas da Ben Kalu, sun kafa ?ungiya, COPSA, wacce a ?ar?ashin ta su ke ta fa?a da Abbas da Ben Kalu da kuma uwar jam’iyya, APC.
Daga cikin masu adawa da Abbas, har da Mataimakin Kakakin Majalisa, Idris Wase, Shugaban Masu Rinjaye, Alhassan Doguwa, Sada Soli, Miriam Onuoha da Muktar Betara.
Dangane da wannan karankatakaliya, Shettima ya ce ya na magana da dukkan hasalallun ‘yan takarar, domin a cimma sasanta sa?anin.
“Zan yi ?o?ari na ga na tuntu?i dukkan sauran masu takara. Shi dai Honorabul Betara ?an uwa na ne. Daga yanki ?aya mu ka fito, kuma daga jiha ?aya mu ka fito. Kuma akwai kyakkyawar ala?a a tsakanin mu. Na gana da shi makonni biyu da su ka gabata. Zan kuma ci gaba da lallashin sa,” cewar Shettima.
Wajen ?arfe 1 na yamma a yau kuma na gana da Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya, Idris Wase. Za mu ci gaba da tuntu?ar juna.”
“Lokacin da Obasanjo ya rasa ta-cewa a majalisa, ai kowa ya shaida yadda zangon sa na farko ya kasance bai yi abin kirki ba. Saboda ru?anin da aka ri?a yi. Ba don komai ba saboda Obasanjo ya yi sakaci Aminu Tambuwal ya zama Kakakin Majalisar Tarayya a lokacin.
“A yanzu ita ma Mariam Onouha akwai sha?uwa tsakani na da ita. Zan tuntu?e ta.”
Shettima ya ce APC ta za?i Godswill Akpabio ne a matsayin wanda su ke so ya zama Shugaban Majalisar Dattawa, saboda ba mu so a ce Shugaban Majalisar Dattawa ma Musulmi ne.
“Mu na so ne mu guje wa yadda za ta kasance shugaba Musulmi, Mataimaki Musulmi kuma Kakakin Majalisar Dattawa ma Musulmi. Kuma Kakakin Majalisar Tarayya shi ma Musulmi, duk addini ?aya. Idan aka yi haka, za a yarda da masu cewa ?o?arin maida Najeriya ?asar Musulunci zalla gaskiya su ke fa?a kenan.
