2023: INEC Za Ta Hada Hannu Da Ma’aikatar Sadarwa Wajen Yada Sakamakon Zabe

A shirinta na ci gaba da ya?a sakamakon za?e kai-tsaye ta intanet a babban za?e na 2023, hukumar za?e ta INEC a Najeriya ta ce za ta gana da hukumar sadarwa ta ?asar a ranar Talata.

Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya fa?a wa editocin kafofin ya?a labarai yayin wata ganawa a Legas cewa ganawar da za su yi za ta ?unshi shugabannin kamfanonin sadarwa hu?u na Najeriya.

Ya ce INEC na ha?a kai da NCC ne don gano kyakkyawar hanyar ya?a sakamakon a kowane lungu da sa?o na ?asar a kan lo?aci.

NCC ce ke kula da dukkan harkokin sadarwa na Najeriya, wadda ke da ?ananan hukumomi a ?ar?ashinta.

Wasu daga cikin jam’iyyun siyasa sun soki INEC game da ya?a sakamakon ta intanet amma ta ce “babu gudu babu ja da baya”.

Related posts

Leave a Comment