Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar kakakin Majalisar Dattawa, Sanata Ajibola Ashiru, ya ce majalisa za ta yi diddigin duba cancanta ko rashin cancantar amincewar su ga Shugaba Muhammadu Buhari ya ciwo bashin dala miliyan 800 kafin saukar sa.
Ashiru ya bada wannan tabbacin ne a ganawar sa da Gidan Talabijin na Channels a ranar Lahadi.
‘Yan Najeriya da dama ba su gamsu da a ciwo bashin ba.
Amma sanatan ya ce kwamitocin da ke da nasaba da harkokin ku?a?e za su gana da hukumomin da abin ya shafa domin tantance alfanu ko rashin alfanun ciwo bashin.
Ya ce daga cikin abubuwan da za su yi la’akari, har da yawan tulin basussukan da ake bin Najeriya, da kuma yiwuwar iya biyan bashin da za a ?ara kinkimowa, a ?ar?ashin Dokar Halastawa da Ta?aita Ciwo Basussuka ta ?asa.
Idan ba a mance ba an wallafa labarin cewa Buhari na neman ciwo bashin dala miliyan 800, duk da gwamnatin sa ta bar Tinubu cikin tsomomuwar ba?in jinin cire tallafin fetur.
Makwanni biyu bayan Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bayyana cewa ta dakatar da cire tallafin mai, har sai lokacin sabuwar gwamnati, duk da haka Buhari ya ro?i Majalisar Dattawa ta amince masa ya ciwo bashin dala miliyan 800 ?in da za a raba wa marasa galihu su miliyan 50, domin tausaya masu halin ?uncin tsadar rayuwar da za su afka, idan aka cire tallafin fetur a ?arshen Yuni.
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ne ya karanta wasi?ar da Buhari ya aika a yau Laraba a zauren Majalisa, saura kwanaki 19 ya sauka daga mulki.
Buhari ya ce za a tura wa talakawa miliyan 50 ?an alawus ?in dannar ?irjin ba su ha?uri su rungumi tsadar fetur, bayan cire tallafi.
Ya ce Majalisar Zartaswa ta rattaba hannun amincewa, yanzu Majalisar Dattawa ka?ai ya ke jira.
