Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar jamiyya mai mulki ta APC, wadda ke marawa Bola Tinubu baya ta lashe zaben jihar Ekiti da yawan kuriu 201,494, sai Atiku Abubakar na PDP da ya samu yawan kuriu 89,554, inda jamiyyar Labour ta Peter Obi ta zo na uku da kuriu 11,397, yayin da NNPP Rabiu Musa Kwankwaso ta samu kuriu 264.
Haka zalika, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Osun.
Atiku ya samu nasara a kananan hukumomi 20 da jimillar kuriu 354,366 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Bola Tinubu na jamiyyar APC, wanda ya samu kuriu 343,945 kuma ya samu nasara a kananan hukumomi 10.
Dan takarar shugaban kasa na jamiyyar Labour, Peter Obi, ya zo na uku a zaben da jimillar kuriu 23,283, sai Rabiu Kwankwaso na jamiyyar NNPP ya samu kuriu 713.

