Shugabancin Kasa: Shugaban Majalisa Ya Bayyana Aniyarsa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan zai fito takarar shugaban ?asa a ?ar?ashin jam’iya mai mulki ta APC.

Lamarin yun?urin fitowar Lawan alama ce ta fitowar wata ‘tauraruwa mai wutsiya’ a cikin ‘yan takarar shugaban ?asa a APC.

Fitowar takarar Lawan zai kasance shi ne ?an takara na biyu daga Arewa, bayan Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi.

Zai ?alubalanci ‘yan Kudu irin su Bola Tinubu, Mataimakin Shugaban ?asa, Yemi Osinbajo, Rotimi Amaechi da sauran su da dama.

Idan ba a manta ba, a ranar Juma’a ce Shugaban APC Abdullahi Adamu ya ce har yanzu APC ba ta tsayar da matsaya takamaimai ba kan kar?a-kar?a, wanda tuni ake gani cewa a tsarin, ?an kudu ne zai yi wa APC takarar shugaban ?asa.

Majiya ta shaida wa wannan jarida cewa Sanata Lawan ya shafe watanni ya na tunani, nazari da tuntu?a domin yiwuwar tsayawar sa takarar shugaban ?asa. Kuma ya na samu daga mutane masu yawa, wa?anda ke matsa masa lambar fitowa takara.

Related posts

Leave a Comment