Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na ?asa, Abubakar Malami ya musanta labaran da su ka ya?u a jiya na cewa ya raba motoci na-gani-na-fa?a ga magoya bayan sa.
Malami ya ?aryata labarin ne a yayin wata ganawa da manema labarai jiya Talata a Birnin Kebbi.
A cewar sa” a kwanakin nan ina shan sharri iri-iri, ta sama, ta ?asa ta tsakiya, wasu a nan cikin gida wasu kuma daga ?asashen waje. Har da sahrrin cewa wai na raba motoci ga masu tsada ga ?an jam’iyar APC.
“A matsayina na mutum mai abokai da dama, ko ni, ko su, babu wanda ya raba wata mota ga kowanne wakilin jami’ya a fa?in jihar nan,” in ji shi.
Malami ya kuma suffanta kabarin a matsayin yarfe da kuma sharri.
Ya kuma yi bayanin cewa shi dai ya san ya gana da shugabannin APC a jihar sakamakon amsa kira da ya yi na al’ummar Kebbi kan ya fito takarar gwamna.
Ya kara da cewa, bayan ganawar, babu wani shugaba ko wakili na jam’iya da a ka baiwa kyautar mota.
