Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dr Isa Ali Pantami ya bukaci masoyansa da ka da su tayar da hankali game da kage da wata jarida ta yi masa na alaka da ta’addanci.
A martanin da ya yi kan zargin, ya ce ka da wani daga cikin magoya bayansa su zagi wani ko su daki wani a madadinsa.
A wani bidiyo da aka ?auka a majalisin karatunsa, shahararren malamin addinin Islama yana cewa; “Duk wanda yake tare dani ban yarda ya zagi wani ba, ban yarda ya yi wa wani kazafi ba, ban yarda ya aibata wani ba, ban yarda ya daki wani ba, ban yarda ya yi komai ba.
“Idan mutum ya yi maganar da ka ga bai dace ba; ka yi masa nasiha. Idan ya zo da labarin da bai dace ba ko gaba da gaba ne ko a rubuce ne kace masa ba haka bane ka gyara. Idan ya dauka fani’ima idan bai dauka ba shi da Allah.
“Ba anan zamu tabbata ba, akwai wata rayuwa bayan wannan ta duniya.”
A makon da ya gabata ne wata jarida ta wallafa cewa, an ga sunan Dr Pantami cikin jerin wadanda ke da hannu a ta’addancin Al-Qa’eeda, lamarin da ya jawo cece-kuce.
