Babbar kotun tarayya da ke Yenagoa, Jihar Bayelsa, ta yanke hukunci cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan zai iya yin takarar shugabancin kasa a zaben 2023.
An alakanta Jonathan da jam’iyyar APC mai mulki a yanzu bayan saya masa fom din takarar shugaban kasa kan Naira miliyan 100.
Sai dai a ranar Juma’a, kotun ta ce Jonathan, wanda ya sha kaye a zaben 2015 a hannun Shugaba Muhammadu Buhari, yana iya neman kujerar shugaban kasar a za?en da 2023 dake tafe.
Mai shari’a Isa Hamma Dashen, wanda ya bada hukuncin a ranar Juma’a, ya ce dokar da aka kafa daga baya ba za ta shafi takarar Jonathan a 2023 ba.
A karar da Andy Solomon da Idibiye Abraham suka shigar, sun nemi kotun ta tabbatar da cewa dokar da aka yi daga baya na hana mataimakan shugaba da suka gaji shugabanninsu yin mulki sau biyu bata shafi Jonathan ba.
Jonathan ya karbi mulki a hannun marigayi Yar’adua ne bayan ya rasu a 2010 kuma ya sake takara a 2011 ya ci zabe.
