Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ?an takarar Shugaban ?asa karkashin jam’iyyar APC Bola Tinubu, tsohon gwamnan Jihar Legas ya ce idan aka zabe shi shugaban kasa, cikin shekaru hudu, zai yi aiki tukuru don ganin an shawo kan matsalar lantarki.
Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a ta bakin hadiminsa Bayo Onanuga, tsohon gwamnan na Legas ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar tana rabar da megawatta na lantarki 15,000 a sassan kasar domin wadata ko ina da hasken wutar lantarki.
“A ?angaren lantarki, zan mayar da hankali don dauka matakin gaggawa nan take don warware kalubalen tashohin samar da lantarki, sayen iskar gas, farashi da rarraba lantarki,”
“Abin da gwamnati za ta saka a gaba shine samar da megawatt 15,000 na lantarki da za a rarraba wa masu amfani da lantarki a sassar kasar don tabbatar da samun lantarki da dauke wa cikin shekaru hudu masu zuwa.”
Tsohon gwamnan na Legas ya kuma ce idan aka zabe shi shugaban kasa, zai kirkiri sabbin hukumomi shida a kowance shiyar kasar da zai mayar da hankali wurin amfani da albarkatun da ke shiyoyin don habbaka su.
