Rahotannin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na bayyana cewar Sanata Kashim Shettima, tsohon gwamnan Jihar ya kwatanta gabatar da Farfesa Babagana Umara Zulum da ya yi a matsayin magajinsa a mafi kyawun matakin da ya taba dauka a tarihin rayuwarsa.
Sanata Shettima ya yi wannan furucin ne a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook bayan Zulum ya lashe zaben fidda gwanin gwamnonin na jam’iyyar APC wanda aka yi a Jihar Borno na zaben 2023.
A shekarar 2019 Zulum ya maye gurbin Shettima kuma a wannan zaben fidda gwanin na APC, Zulum ne kadai dan takarar gwamna. An yi zaben ne a Cibiyar Wasannin Elkanemi da ke Maiduguri ranar Alhamis.
“A yau ni ne mutumin da ya fi kowa murna a doron kasa, saboda kamar kullum, tun bayan da na bar ofis, Ubangiji ya ci gaba da wanke ni. “A 2018, kai (Zulum) tare da wasu mutane tara ku ka yi takarar neman gwamnan Jihar Borno na zaben 2019, amma bayan ganin salon mulkinka cike da gaskiya da jajircewa yanzu babu wanda ya fito ya kara da kai.
“Matakin da na dauka a 2018 na gabatar da kai a matsayin magajina shi ne mafi kyawun yanke shawarar da na taba yi. Ban yi nadama ba kuma da zan kara samun irin damar zan ci gaba da zabenka.”
