Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ‘Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce wa jam’iyya mai mulki dubunta zai cika a zaben 2023.
Atiku ya ce jam’iyya mai mulki ta APC ta gaza bayyana damuwarta game da wadanda ‘yan ta’adda suka kai wa farmaki a Owo, jihar Ondo yayin da gaba daya kasar ke cikin jimami.
Sannan ta gaza fasa gabatar da taro da ‘yan takarar shugaban kasarta a ranar da aka kai harin, inda ya siffanta hakan da halin ko in kula da rashin iya shugabanci.
A wata takarda da hadimin ?an takarar shugaban kasar jam’iyyar PDP, Paul Ibe, ya fitar a ranar Litinin ya bayyana abubuwan dake faruwa a matsayin wata babbar alama dake nuna rugujewar APC.
A cewar Atiku, ba dalili bane a ce don ana gabatar da zaben fidda gwanin jam’iyyar duk da rahoton da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya samu amma duk da haka ya samu kwarin guiwar zaben wanda zai gajeshi.
“Duk da yadda jinin bayin Allah ke kwarara a titin jihar a tsakar rana, hakan bai hana shugabannin jam’iyyar APC taruwa a Abuja tare da gabatar da taron a cikin wani yanayi da ke bayyana rashin tausayin kasa,” a cewarsa.
“Har ila yau, abin takaicin da APC ta kira da zaben fidda gwani wanda kawai na?a ?an takara aka yi, yana da kyau a tambaye shugabannin jam’iyyar dalilin da yasa suka zabi gabatar da abun da suke kira da zaben fidda gwani a cikin ranakun aiki, wanda hakan ya dagula lamurran tattalin arzirki a cikin birnin tarayyar.
“Ko da wakilan zabe a abin da suka kira da zabe suka shiga babban birnin tarayyar, sun fuskanci dogon layin siyan man fetur da duhun da ya cigaba da dawainiya da babban birnin saboda rashin wutar lantarki,”
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce mazauna birnin tarayyar wadanda suka dade suna fuskantar tsananin rayuwar yau da kullum sanadiyyar shugabanci mara kyau na jam’iyya mai mulki, zabar mahimman ranakun aiki – Litinin da Talata – saboda zaben fidda gwanin APC alama ne na son zuciya.
