Shugabancin Kasa: Atiku Ya Fi Karfin Tinubu – PDP

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar, babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce tana jin tausayin tsohon gwamnan Jihar Lagos Bola Tinubu wanda APC ta tsayar takarar shugaban kasa a zaben 2023.

A wata sanarwa da PDP ta wallafa a shafinta na Tuwita bayan an bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwani na shugaban kasa a APC, ta ce abin takaici ne yadda ya samu tikitin takara a jam’iyyar da ba ta tsinana wa ‘yan kasar komai ba.

“Jam’iyyarmu tana kuma tausaya wa Asiwaju bisa bin hanyar da ba za ta bille ba domin kuwa shi ba sa’an dan takarar PDP Atiku Abubakar bane, wanda ya fi kwarewa da kuma shiryawa wajen zaman shugaban kasa in ji PDP.

Siyasar Najeriya ba irin ta Jihar Lagos ba ce inda ta yi zargin cewa Bola Tinubu yana amfani da karfi wajen tursasa wa jama’a.

Related posts

Leave a Comment