Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka yi a ranar Laraba.
Kwankwaso ya yi nasarar zama dan takarar shugaban kasar na NNPP ne bayan daligets 774 daga jihohi 36 sun sahale masa gaba daya ba tare da hamayya ba.
Idan za a iya tunawa, shugaban jam’iyyar na NNPP na kasa, Boniface Aniegbonam, ya ce Kwankwaso shine dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a shekarar 2023 a yayin taron manema labarai a Legas a ranar Juma’a da ta gabata.
Kwankwaso shine gwamnan Jihar Kano daga shekarar 1999 zuwa 2003 sannan ya sake yin gwamna daga 2011 zuwa 2015.
Bayan ya fadi zabe a 2003, an nada shi Ministan Tsaro a Jamhuriya ta hudu. Daga bisani an zabe shi sanata a karkashin jam’iyyar APC mai wakiltar Kano ta tsakiya a majlisar dattawa.
