Adamawa: An Cafke Katon Dake Shigar Mata A Dakin Dalibai Mata

Rundunan ‘Yan Sandan Jihar Adamawa ta yi nasarar kama wani matashi mai yin shigar Mata wanda kuma ya kan shiga ?akin kwanan Mata domin yin sata a makarantar horar da Unguwarzoma dake Yola.

Matashin mai suna Jika John ya tabbata da lafinsa a zantawarsa da manema labarai a hedkwatar rundunan ‘yan Sanda dake Yola.

Da yake yi wa manema labarai jawabi CSP Ahmed D Gombi a madadin Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP S.K Akande yace Matashin tare da abokan aikinsa wanda ba a kai ga kama su ba yana basu karin haske kan yadda suke gudanar da ayyukansu don kuwa sun yi ?aurin suna wajen gudanar da irin wanannan aika aika.

CSP Ahmed ya kuma kira yi al umma dake fadin jahar Adamawa da su kasance masu taimakawa rundunar da bayanan sirri wanda hakan zai ba rundunan damar dakile ayyukan ta’addanci a fadin jihar baki daya.

Related posts

Leave a Comment