Kyari: Jahiltar Shari’a Ya Sa Dilalan Hodar Iblis Bada Shaida – Lauya

Babban Lauya kuma tsohon Antoni Janar na Najeriya, Kanu Igabi wanda shine lauyan Abba Kyari, ya shaida wa kotu cewa idan aka yi gaggawar yanke wa dillalan da su ka amsa laifin su hukunci, to hakan na iya shafar shari’ar da ke wa Abba Kyari da sauran ‘yan sanda hu?u da ba su amsa laifin su ba.

Igabi ya yi wannan bayani ne jim ka?an bayan da lauyan NDLEA Joseph Sunday ya ro?i kotu da ta fara shirin shari’ar biyu ?in da su ka amsa laifin su domin a yanke masu hukunci nan gaba ba tare da ?ata lokaci ba.

Sai dai kuma Kanu Igabi ya nuna damuwa cewa, ba mamaki wa?anda “suka amsa laifin su ?in sun amsa ne a cikin rashin sanin shari’a.”

Lauyan wa?anda su ka amsa laifin su ?in mai suna Mista Okenyi ya ce ba su amsa laifin su a cikin rashin sanin shari’a ba, domin har sassauci su ka nemi kotu ta yi masu, bayan sun amsa laifin su.

Mai Shari’a Emeka Nwite ya ?age shari’ar zuwa ranakun 14 da 28 Ga Maris, domin tattauna batun beli.

Related posts

Leave a Comment