Shugabancin APC: Ku Amince Da Dan Takara Guda – Kiran Buhari Ga ‘Yan Takara

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya roki ?an takaran shugabancin jam’iyyar APC da su daidaita a tsakanin su su fidda mutum ?aya.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a wajen taron ganawa da yayi da duka ?an takaran shugaban jam’iyyar su 7 a fadar Aso Rock.

” Abinda na ke so shine mu ha?u dukkanmu mu ha?a kai maimakon ayi ta jani-in-jaka, a amince wa mutum ?aya shikenan ba tare da an fantsama zabe ba.

Bayan haka Shugaban ya umarci jam’iyyar ta maida wa duk wanda ya janye ku?in fom ?in sa da ya saya.

Baya ga Abdulaziz Yari da ya yi wa tsarin jam’iyyar tirjiya yayi gaban kan sa duk da tsarin da akayi na ?an yankin Arewa Ta tsakiya ne zai yi takaran shugaban Jam’iyyar, duka sauran yan yankin da jam’iyyar ta tsara ne.

Sanata Abdullahi Adamu daga Jihar Nasarawa da Tanko Almakura na jihar ne ke kan gaba wajen yin nasara a zaben shugaban.

Bayan su akwai tsohon gwamnan Benuwai, George Akume, sannan kuma akwai Mohammed Eksu.

Buhari ya kuma umarci gwamnoni su tattara sunayen wa?anda suke ganin sune suka dacewa kuma aka yarda dasu gaba daya kawai a amince da su ba sai an kai ga yin za?e ba.

Related posts

Leave a Comment