Somaliya: Mayakan Al-Shabab Sun Hallaka ‘Yar Majalisa

Rahotannin dake shigo mana daga kasar Somaliya na bayyana cewar a kalla mutum 15, ciki har da wata ‘yar majalisar kasar sun halaka, bayan da wasu ‘yan kunar bakin wake suka kai hare-hare biyu a garin Beledweyn na tsakiyar kasar.

Firaminista Mohamed Hussein Roble ya bayyana kashe Amina Mohamed Abdi a matsayin “kisan gilla”. Shi kuma shugaban kasar Abdullahi Farmajo ya aika da sakonsa na ta’aziyyar ta Twitter:

Cikin mamatan akwai tsohon dan majalisa Hassan Dhuhul da wasu sojojin Somaliya.

Kafofin yada labarai a yankin na cewa yawan mamatan na iya zarce alkaluman wadanda aka sanar a yanzu.

Babbar tashar talabijin ta Somaliya ta wallafa wasu hotuna na wadanda aka kashe yayin harin.

Kungiyar Al-Shabab ta dauki alhakin kai hare-haren – wadanda aka kai a biranen Mogadishu da tsakiyar Beledweyne.

Related posts

Leave a Comment