Shugaban Kasa Ya Dawo Gida Najeriya

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koma Abuja, babban birnin tarayya daga Birtaniya bayan kwashe kwana 18 a kasar.

Shugaban kasar ya isa Abuja da yammacin Juma’a bayan ya halarci taro kan ilimi a kasashen duniya wanda Firaiministan Birtaniya Boris Johnson da shugaban Kenya Uhuru Kenyatta suka jagoranta.

Daga bisani likitoci sun duba lafiyar shugaban na Najeriya.

Manyan jami’an gwamnati da ministoci na ciki wadanda suka tarbi Shugaba Buhari bayan isarsa filin jirgin saman Nnamdi Azikwe.

Related posts

Leave a Comment