Domin murnar shiga wannan sabuwar shekarar Musulunci ta 1443 bayan Hijra, wasu jihohin Najeriya sun bada hutu ga al’ummarsu, domin girmama wannan muhimmiyar Shekara.
Rahotanni daga birnin Kano na bayyana cewar Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya alanta ranar Litinin, 9 ga Agusta, a matsayin ranar hutu don murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci – Hijrah 1443.
Wannan na kunshe cikin jawabin da kwamishanan labaran, Muhammad Garba, ya saki ranar Juma’a 4. Jihar Jigawa Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da ranar Litinin, 9 ga Agusta, a matsayin ranar hutu don murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci
Ya yi kira ga mutanen jihar suyi amfani da wannan dama wajen yiwa jihar addu’a da kasa baki daya a kan halin rashin tsaron ake ciki.
Jihar Osun Gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola, ya sanar da ranar Litinin, 9 ga Agusta, a matsayin ranar hutu don murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci – Hijrah 1443 AH.
Wannan na kunshe cikin jawabin da Kwamishanan harkokin cikin gidan jihar, Tajudeen Lawal, ranar Juma’a a Osogbo, rahoton NAN.
Jihar Oyo Gwamnatun jihar Oyo, ta sanar da ranar Talata, 10 ga watan Agusta, a matsayin ranar hutu don murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci – Hijrah 1443 AH.
Wannan na kunshe cikin jawabin da Sakataren gwamnatin jihar, Mrs Olubamiwo Adeosun, ta saki ranar Juma’a a Ibadan, babbar birnin jihar.
Gwamnan ya yi kira ga Musulmai da masu bin sauran addinai suyi amfani da hutun domin addu’a ga cigaban jihar da Najeriya gaba daya.
Jihar Kebbi Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu ya bi sahun takwararorin na bada hutun sabuwar shekarar Musulunci. Wannan na kunshe cikin jawabin da aka saki a birnin Kebbi.
