Babban hafsan sojin Najeriya Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya rasu sakamakon hadarin jirgin saman soji a Kaduna.
Mai magana da yawun rundunar sojin, Birgediya Janar Mohammed Yarima ne ya tabbatar da faruwar lamarin.
Bayanai sun ce jirgin saman na soji ya fadi ne a kusa da filin tashi da saukar jiragen sama na Kaduna kuma mutum takwas ne a cikin jirgin lokacin da lamarin ya faru.
Rundunar sojin saman Najeriyar ta wallafa wani sa?o a shafinta na Twiiter inda ta bayyana cewa wani jirginta ya fa?i a kusa da filin jirgin sama na Kaduna.
Ta kuma ce tana bincike kan abin da ya haifar da ha?arin.
Laftanar Janar Ibrahim Attahiru shi ne ya maye gurbin Janar Tukur Buratai babban hafsan sojan ?asa.
An haifi Janar Attahiru a 1966 a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Ya taba jagorantar ya?i da ?ungiyar Boko Haram amma a shekarar 2017 ne Janar Tukur Buratai ya sauke shi daga mu?amin bayan wasu hare-hare da ‘yan bindiga suka kai inda aka kashe wasu mutane 50 a lokacin da suke sallah a masallaci.
Kafin ba shi wannan mu?amin, Laftanar Janar Attahiru shi ne shugaban runduna ta 82 a rundunar sojin Najeriya.
Ranar 26 ga watan Janairun 2021 ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya na?a shi a matsayin Babban Hafsan Sojin ?asar.
Janar Attahiru shi ne babban Hafsan Sojin Najeriya na 21.

Wannan ne ha?arin jirgin sojin saman Najeriya na uku cikin wannan shekarar ta 2021.
A watan Janairu wannan shekarar ma wani jirgin rundunar ya fa?i a kusa da filin jirgin sama na Abuja babban birnin Najeriya.
Haka kuma, ran 31 ga watan Maris rahotanni suka bayyana cewa akwai jirgin rundunar da ya yi ?atan dabo a jihar Borno, kuma bayan ?an kwanaki rundunar ta sanar da cewa akwai yiwuwar jirgin nata fa?uwa ya yi.
An fitar da sunayen wadanda Hatsarin Jirgin ya rutsa da su kamar haka….
- LT GEN I ATTAHIRU.
- BRIG GEN MI ABDULKADIR.
- BRIG GEN OLAYINKA.
- BRIG GEN KULIYA.
- MAJ LA HAYAT.
- MAJ HAMZA.
- SGT UMAR.
CREW
- FLT LT TO ASANIYI.
- FLT LT AA OLUFADE.
- SGT ADESINA.
- ACM OYEDEPO.
The COAS was on his way to Depot NA for tomorrow POP
