Yadda Hatsarin Jirgin Sama Ya Ci Ran Shugaban Dakarun Soji

Mai magana da yawun rundunar sojin, Yerima Mohammed ne ya tabbatar da faruwar lamarin da yammacin ranar yau Juma’a.

Tun da fari Rundunar sojin saman Najeriyar ta wallafa wani sa?o a shafinta na Twiiter inda ta bayyana cewa wani jirginta ya fa?i a kusa da filin jirgin sama na Kaduna.

Ta kuma ce tana bincike kan abin da ya haifar da ha?arin.

Wane ne Janar Attahiru?

Manjo Janar Ibrahim Attahiru shi ne ya maye gurbin Janar Tukur Buratai babban hafsan sojan ?asa.

Janar Attahiru ?an asalin jihar Kaduna ne a arewacin Najeriya.

Kafin ba shi wannan mu?amin, Manjo Janar Attahiru shi ne shugaban runduna ta 82 a rundunar sojin Najeriya.

Ya taba jagorantar ya?i da ?ungiyar Boko Haram amma a shekarar 2017 ne Janar Tukur Buratai ya sauke shi daga mu?amin bayan wasu hare-hare da ‘yan bindiga suka kai inda aka kashe wasu mutane 50 a lokacin da suke sallah a masallaci.

Dama dai Buratai ya ba shi wa’adin kamo shugaban Boko Haram Abubakar Shekau a mace ko a raye.

Janar Nicholas Rogers ne ya maye gurbinsa

Related posts

Leave a Comment