Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babban Baturen’yan Sanda na ?asa, Usman Al?ali Baba, yace babu wani abun tsoro kan barazanar da Boko Haram ta yi na kawo hari Abuja da Jihar Filato.
Kakakin hukumar yan sanda, Mr Frank Mba, shine ya bayyana haka a wani sa?o da ya fitar ranar Juma’a a Abuja, domin mayar da martani akan labaran da ake ya?awa na cewar Boko Haram na barazanar kawo hari a birnin tarayya Abuja.
Kamfanin dillancin labarai na ?asa (NAN) ya gano wani rahoton sirri dake nuni da cewa, sufetan yan sanda ya ba kwamishinan ‘yan sanda na jihar Plateau da takwaransa na Abuja umarnin su ?auki matakin da ya dace domin da?ile duk wani hari da za’a kawo yankunan su.
Ya bu?ace su da su kare muhimman kayayyakin gwamnati dake yankin su biyo bayan gano shirin maya?an Boko Haram na kai hari. Sai dai kakakin hukumar yan sandan ya bayyana cewa wannan umarnin ba yana nufin akwai wata barazanar kawo hari a biranen biyu bane.
Yace an ba kwamishinonin biyu umarnin ne don su ?ara shiri wajen dakile duk wata barazanar kawo hari daga yan ta’adda a yankunan su. A cewarsa, anyi hakan ne don a ?ara tabbatar da doka a wa?annan garuruwan kuma a kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu.
“Umarnin ba yana nufin an san cewa za’a kawo hari a jihohin biyu bane kamar yadda wasu ke ya?a wa.” inji kakakin yan sandan. Ya kuma ro?i mazauna wa?annan jihohin biyu su kwantar da hankalinsu, su cigaba da gudanar da ayyukan su na yau da kullum.
