Salon Mulkin Buhari Ne Ya Sa Ake Tsanar Fulani A Najeriya – Lami?o

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar adawa ta PDP, Alhaji Sule Lamido ya ce duk wani wulakanci da Fulani ke fuskanta a yankin Kudu shugaba Muhammad Buhari ne sila saboda irin yadda yake tafiyar da mulkinsa.

Sannan kuma ya dora laifin kan wasu daga cikin jigogin jam’iyyar APC na Kudu Irinsu Tinubu, Amaechi, Fashola, Cris Ngige, Rochars da sauransu.

Ya ce sun taimaka wa Buhari ya ci zabe amma sun kasa wayar da kan al’ummar su cewa ba duka Fulani ba ne bata gari.

Al’ummar Fulani na cigaba da fuskantar kyama da suka a tsakanin sauran ?abilun Najeriya, sakamakon yadda ake yawaitar samun masu aikata miyagun ayyuka a cikin su.

A baya bayan nan Mai alfarma Sarkin Musulmi Dr Sa’adu Abubakar ya bayyana wa duniya cewa ba Fulani ka?ai ba ne ke aikata ta’addancin da ke faruwa a Najeriya akwai sauran ?abilu da ke da hannu a ciki, saboda haka a daina yin ku?in horo.

Related posts

Leave a Comment