Gobe Ne Sallah: Ba A Ga Jinjirin Wata A Najeriya Ba – Sarkin Musulmi

Rahotannin dake shigo mana daga birnin Sokoto na bayyana cewar Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad III ya sanar da cewa bayan duban wata da aka yi a fadin tarayya, ba’a ga jinjirin watan Shawwal a Najeriya ba.

Sarkin ya ce sakamakon haka za’a da azumi don watan Ramadan ya cika Talatin (30) kuma ayi Sallah ranar Litinin 2 ga watan Mayu, 2022.

Rahotanni sun bayyana cewa kwamitin duban wata na majalisar koli ta addinin Musulunci ya bayyana cewa kawo karfe 7:35 na daren Asabar an samu rahotanni daga jihohi bakwai na rashin ganin Wata.

Dukkanin rahotannin sun nuna cewa ba’a ga jinjirin wata ba. Wadannan jihohi sun hada da Misau jihar Bauchi, Sokoto, Kaduna, Lagos, Ilorin, Abuja da Abeokuta na Jihar Ogun.

Related posts

Leave a Comment