Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Adam Namadi, dan tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Namadi Sambo, ya nemi wakilan zabe wato daligets su dawo masa da kudin da ya ba su bayan rasa tikitin takara.
Wannan na zuwa ne yayin da zaben fidda gwanayen takara na jam段yyar PDP ke ci gaba da gudana a fadin kasar.
An ruwaito cewa Adam ya sha mugun kaye ne bayan samun kuri置 biyu kacal a zaben fidda gwanin takara na dan majalisa mai wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa a Tarayya.
Gabanin hakan dai Adam ya ba wakilan zaben Naira miliyan biyu-biyu da zummar su kada masa kuri誕r tsayar da shi a matsayin dan takarar kujerar Majalisar Wakilai naazabar Kaduna ta Arewa.
Haka kuma, dan tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya yi alkawarin kara wa wakilan zaben Naira miliyan daya da rabi-rabi domin samun nasara, amma shi ne ya tashi da kuri置 marasa yawa duk cikin manema takarar kujerar.
Tuni dai su kuwa wakilan zaben suka cika lalitarsu da miliyoyin naira daga aljihun manema takarar da suka fito kwansu da kwarta da zumudin ganin sun yi galaba a kan abokan karawarsu.
A karshe dai Sama段la Suleiman, dan majalisar Kaduna ta Arewa mai ci a yanzu shi ne ya sake lashe zaben, inda ya tika Adam Namadi da kuma Shehu Usman ABG da kasa.
Sama段la Suleiman wanda a kwanan nan ya sauya sheka daga jam段yyar APC zuwa PDP, ya samu kuri置n wakilan zabe 22 yayin da Shehu Usman ABG ya samu 14.
Wakilan zaben sun shaida wa Aminiya cewa Sama段la Suleiman ya rarraba musu kudi daga kan naira miliyan 3.5 zuwa miliyan 4, yayin da shi kuwa ABG ya danka musu Naira miliyan 2.5, inda Adam Namadi ya rarraba musu naira miliyan biyu kacal.
Sai dai bayan shan kasa, ABG da Adam Namadi sun bukaci wakilan zaben su gaggauta dawo musu da kudadensu.
