2023: Ba Na Neman Kujerar Mataimakin Shugaban Kasa – Zulum

Gwamnan jihar Barno Babagana Zulum ya bayyana cewa ba ya bibiyan wani dan takarar shugaban Kasa ya nada shi mataimakin shugaban kasa.

Zulum ya kara da cewa babu wani dan takara da jihar tayi wa alkawarin za ta bashi kuri’un ta a zaben fidda gwani.

“Dalili kuwa shine mulki Allah ke bada shi saboda haka babu wani, duk wanda Allah ya ba shi ne za mu bi, amma mu ba mu isa mu ce ga wanda zai zama shugaban kasa ba dole.

” ‘Yan Najeriya sun shiga cikin matsi da tsananin gaske sannan ga ba?in talauci da ake fama da shi. Dole sai an maida hankali wajen kawo karshen hakan za a cigaban da ake nema.

” Sannan kuma dole a maida hankali wajen yaki da da rashawa, ya kamata a ?auki wannan abu da mahimmanci idan aka yi haka ne kawai za a samu nasara a kasar nan.

Related posts

Leave a Comment