Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ?an takarar Sananta jam’iyyar APC Muhammad Sani Abdullahi, ya gabatar da shaidu shida domin ?alubalantar nasara da takardun ?an takarar PDP, Lawal Adamu wanda aka fi sani da Mr LA.
Kotun mai al?alai uku a ?ar?ashin jagorancin mai shari’a HH Kereng, ta saurari bayanan shaidun wa?anda suka fito daga makarantun da ?an takarar PDP ya halarta da hukumar shirya za?e ta INEC.
Shaidun APC 6 sun bayar da shaida akan ?an takarar PDP kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta yi rahoto cewa jami’ar Ahmadu Bello, Zaria (ABU) ita ce ta fara bayar da shaida inda ta samu wakilcin ?aya daga lauyoyinta, Abubakar Is’haq daga tsangayar ilmin shari’a na jami’ar.
An gayyato jami’ar ne domin ta bayar da takardun bayanan Lawal Adamu lokacin da yake matsayin ?alibi a jami’ar. Shaida ta biyu, hukumar shirya jarabawa ta ?asa (NECO) wacce ta samu wakilcin darektan ayyukan na musamman Esther Bala Wuyaa, ta gabatar da ha?i?anin takardar da ke tabbatar da sakamako a gaban kotu.
Shaida ta uku shi ne shugaban makarantar Demonstration Primary School, Dr. Ibrahim Yusuf, wanda ya gabatar da rajistar makarantar daga 1982 zuwa 1986 wanda ya nuna babu bayanan Lawal Adamu Usman a matsayin ?alibin makarantar.
Da yake bayar da shaida a gaban kotun, shugaban makarantar sakandiren Government Day Secondary School (GDSS), Gwagwalada, Bello Suleiman, ya ce babu bayanan Lawal Adamu Usman a matsayin ?alibin makarantar daga 1986 zuwa 1994 kamar yadda yake i?irari.
An kuma kira ?arin wasu shaidu biyu ciki har da na hukumar INEC wa?anda suka gabatar da shaidunsu a gaban kotu. Kotun ta kar?i bayanansu a matsayin shaida Dukkanin makarantun da suka bayar da shaida sun mi?a takardun rajistarsu ga kotun a matsayin shaida. Kotun ta ?age sauraron ?arar har sai zuwa ranar, 11 ga watan Yulin 2023 domin ci gaba da kar?ar shaidu kan ?arar satifiket ?in bogi da ake yi wa wanda ake ?ara.
