Rahotanni daga birnin Riyadh na ?asar Saudiyya na bayyana cewar kasar ta zartar da hukuncin kisa kan mutum 81 a rana ?aya bayan samunsu da laifukan da suka shafi ta’addanci, kamar yadda kamfanin dillacin labaran ?asar SPA ya ruwaito.
Wannan ya zarta adadin mutanen da aka zartarwa hukuncin kisa a bara.
Mutanen sun ha?a da wa?anda aka samu da laifin suna da ala?a da Al Qaeda da IS da kuma maya?an Houthi da ke ya?i a Yemen.
Wa?anda aka kashe suna shirin kai hare-hare a Saudiyya – da ko?arin kashe fararen hula da jami’an tsaro, kamar yadda kamfanin dillacin labaran Saudiyya SPA ya ruwaito.
Mutum 73 daga cikin 81 ?an asalin Saudiyya ne, bakwai kuma ?an Yemen da kuma mutum daya ?an ?asar Syria.
