Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya yi garga?i ga shugabanni da ?an jam’iyar APC da su daina nuna wa juna yatsa da sa-in-sa a junansu, yayin da jam’iyar ke tunkarar babban taron ta na ?asa a ranar 26 ga watan Maris.
An ruwaito cewa APC ta sake nutsa wa cikin rikici bayan da gwamnoni 19, ?ar?ashin jagorancin Gwamna Nasir El-Rufai su ka ham?arar da kujerar shugaban kwamitin ri?o na jam’iyar, Gwamna Mai Mala Buni, inda a ke zargin da umarnin shugaban ?asa su ka aikata hakan.
Daga bisani sai Buhari ya ja kunnen ?an jam’iyar da su ci gaba da jajirce wa da ha?a kai domin jam’iyar ta ci gaba da tafiya a kan gwadabenta na nasara da ta ke kai.
Buhari ya kuma buga misali da jam’iyar adawa ta PDP, inda ya ce duk karfin ta a ?asar nan amma yanzu ta yi ?asa.
A sanarwar da kakakin sa Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce APC ta kwashe kusan shekaru 8 tana mamaye sauran jam’iyyu sabo da ta bu?e kofar ta ga duk wanda yanke so ya shigo da ga wata jam’iya, babba ko karama.
