Kaduna: An Sake Dage Zabukan Kananan Hukumomi

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Shugaban hukumar zaben jihar Kaduna (SIECOM) Dr. Saratu Dikko Audu ta bayyana ?age zaben kananan hukumomin jihar zuwa ranar 4 ga watan Satumban 2021.

Ta bayyana hakan ne a hedkwatar hukumar a wani taro da suka yi ranar Litinin a Kaduna kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An ruwaito yadda aka tsara zaben shugabannin kananan hukumomi 23 da kansiloli ya zama ranar 5 ga watan Yuni 2021 kafin a dage zuwa 14 ga watan Augusta, sannan zuwa 4 ga watan Satumba.

Related posts

Leave a Comment