Rahotannin daga Riyadh Babban Birnin Kasar Saudiyya na bayyana cewar Hukumomi sun ce a?alla masu ibada miliyan 14 suka ziyarci Masallacin Annabi SAW a Madina tun farkon soma azumin watan Ramadan, kamar yadda kamfanin dillacin labaran ?asar ya ruwaito.
Hukumomin sun ce dun ?auki matakai na lafiya sakamakon yawan masu ibadah a bana. Kuma sun ce zuwa yanzu babu ?arkewa wata annoba ko cuta ko wani abin da ke barazana ga lafiya.
Hukumomin sun ce ma’aikata 18,000 ke aikin kula da masu ibadah a Masallacin.
