Mutuwar Alafin Na Oyo Rashi Ne A Najeriya – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa gwamnatin Jihar Oyo da al’ummar jihar kan rasuwar sarkin Yarabawa Alafin na Oyo, Lamidi Olayiwola Adeyemi III, ranar Juma’a.

Buhari ya bayyana shekara 52 da sarkin ya shafe a karagar mulki da “masu ?ayatarwa ta hanyoyi da dama” cikin wata sanarwa da kakakin fadar shugaban ?asa Femi Adesina ya fitar.

A ranar Asabar aka yi jana’izar sarkin a tsohon garin Oyo, inda aka binne shi a farfajiyar masarautarsa.

Mai martabar ya rasu ne yana da shekara 83 a wani asibiti da ke Jihar Ekiti bayan ya yi fama da jinya.

Related posts

Leave a Comment