Duk da ba hukumomin tsaro umarni har sau 29 cikin shekaru uku domin kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda, ‘yan Najeriya na ci gaba da rayuwa cikin fargaba sakamakon asarar rayuka da dukiyoyi da ake samu akai-akai.
Wasu ‘yan Najeriya da masana harkokin tsaro na zargin tabarbarewar tsaro da rashin kishin kasa daga bangaren gwamnati yayin da wasu ke cewa galibin umarnin ba daga shugaban kasa ba ne kai tsaye.
An ruwaito cewa, bayan duk wani hari da aka kai wa ‘yan Najeriya da ko kuma a kan wata hukuma, fadar shugaban kasa kan fitar da sanarwar yin Allah wadai da umartar hukumomin tsaro da su bi bayan maharan kuma kada su bari a sake faruwar lamarin.
Sai dai kuma, a mafi yawan lokuta, masu aikata laifukan kan kara aikata ta’asa jim kadan bayan kowanne umarnin shugaban kasa.
Duk da cewa a ‘yan kwanakin da suka gabata sojoji da wasu jami’an tsaro sun samu wasu nasarori ta hanyar kawar da ‘yan ta’addan Boko Haram da ‘yan bindiga da dama, wasu masana sun ce ‘yan Najeriya na bukatar karin jajircewa daga wajensu domin kawo karshen tada kayar baya a kasar da ta shafe sama da shekaru goma ana tafkawa
