Gwamnatin Tarayya Za Ta Kashe Biliyan 30 Wajen Gyaran Majalisa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta ce gyare-gyaren da za a yi a majalisar Najeriya zai ci Naira Biliyan 30.2 domin sake dawo da majalisar cikin hayyacinta.

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Musa Mohammad Bello, ya shaidawa manema labarai irin kudin da wannan aiki zai lakume.

Naira Biliyan 37 aka ware a kasafin kudin 2020 domin gyara majalisa, amma daga baya dole aka rage kudin zuwa Naira biliyan 9.25 a tsakiyar shekara.

Musa Mohammad Bello ya sanar da kwamitin majalisar dattawa cewa asalin kudin aikin shi ne Naiara biliyan 30.2, an biya ‘yan kwangila Naira biliyan 9.2. Ministan ya fadawa Sanatoci cewa a ranar 15 ga watan Agustan 2023 za a kammala wannan aiki da aka fara tun a ranar 16 ga watan Afrilun shekarar nan.

Related posts

Leave a Comment