Tsohon ?an Majalisar Wakilai mai wakiltar ?ananan Hukumomin Kiru da Bebeji, Abdulmuminu Jibril Kofa, ya sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar APC.
Kofa, wanda shine kuma Daraktan Ya?in Za?en Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da hakan ne a sahihin shafinsa na Facebook a yau Asabar.
A takaitaccen sakon da ya wallafa, Kofa ya ce ya yi iyaka ba?in ?o?arinsa a kan jam’iyyar APC, saboda haka lokaci yayi da zaiyi gaba a siyasar sa.
ya kuma ?ara da cewa cikin awanni 24 zai sanar da makomar sa a siyasa.
“Nayi wa APC iya kokari na lokaci yayi da zan yi gaba. Zan sanar da sabuwar jamiyyar da zan shiga cikin sa’oi 24 In sha Allah. Zanyi cikakken bayani bada jimawa ba,” in ji shi.
