Kotun Amurka Ta Ayyana Ranar Saurarar Shari’ar Kyari

Labarin dake shigo mana daga ?asar Amurka na bayyana cewar Kotun ?asar ta canza ranar gurfanar da Abba Kyari, dakataccen jami’in ?an sanda da wasu mutumn biyar, bisa zarginsu da shiga sar?akiyar damfarar $1.1 miliyan da Romon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi ya jagoranta.

Kotun yankin Amurka ta tsakiyan California ta sake canza ranar gufanarwan daga watan Mayu zuwa watan Oktoba, 2022, duba da bu?atar da uku daga cikin wa?anda ake tuhuma tare da Kyari suka shigar.

Wannan ya zo ne ana tsaka da bada?ala, bayan shigar da ?arar Abba Kyari a gaban kotun tarayya dake Abuja da NDLEA ta yi, bisa zarginsa da safarar hodar- iblis.

An ruwaito a watan Satumbar shekarar da ta gabata yadda bangarorin suka shigar da bu?atar ?age sauraran ?arar don bai wa mutane ukun damar shiryawa shari’ar.

Yayin sauraron ?arar a 29 ga watan Maris, 2022, Al?alin Otis Wright ya amince da cewa, ?in biyawa ?angarorin bu?atarsu na iya zama sanadin “hana tawagar dake kare kansu isashshen lokacin da ya kamata su shirya wa shari’ar yadda ya da ce.”

Ya ?ara da cewa “hakan zai iya haramtawa masu kare kansu cigaba da kare kansa” sannan ya zama dalilin “Haifar da ?a mai ido ko gazawa wajen yin adalci” idan kotun ta ?i amincewa da bu?atar ?age sauraron ?arar.

Saboda haka ne, Al?alin ya ?age sauraron ?arar daga 17 ga watan Mayu, 2022, har zuwa 11 ga watan Oktoba, 2022. “Masu kare kansun za su bayyana a dakin shari’a 5D na kotun tarayya mai lamba 359W, titin farko, Los Angeles na Califonia a ranar 11 ga watan Oktoba, 2022, da karfe 9:00 na safe,” bisa umarnin da alkali ya zartar.

Related posts

Leave a Comment