A fili yake da akwai gagarumin banbanci a tsakanin mai girma Alhaji Isa Ashiru Kudan da sauran ‘yan takara dake han?oron hawa Kujerar gwamnan jihar Kaduna a shekarar 2023.
Idan ana magana ta fuskar gogewa da cancanta Isa Ashiru Kudan ya sha gaban dukkanin sauran ‘yan takara walau wa?anda suka fito a Jam’iyya guda da su ta PDP ko kuma wa?anda suke a sauran jam’iyyu.
Masana ilimin siyasar duniya sun yi ittifaki akan cewa shugaba nagari dole zai kasance wanda ya cika wasu sharudda a rayuwarsa wa?anda suka ha?a ilimi na zamani da na addini da kuma ilimin zamantakewar rayuwa.
Dukkanin wadannan sharudda mai girma Sarkin Bai na Zazzau Alhaji Isa Ashiru Kudan ya cika su ya yi wa saura fintinkau.
Batun taimako da gina al’umma sun zama tamkar al’ada ce a wajen Isa Ashiru Kudan, adadin mutane Maza da Mata wa?anda ya taimaka musu suka ginu har suke gina wasu daga kowane sashe a fadin Jihar Kaduna mai kananan hukumomi 23 ba su lissafuwa.
Jama’ar jihar Kaduna Shaida ne dangane da irin ?wanji da ?an siyasar ya nuna a lokacin da yake za?a??en ?an Majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Kudan da Ma?arfi, ya zama wani tauraro tsakanin sauran ‘yan Majalisar yankin arewa da ma ?asa gaba ?aya.
Wannan shi ne babban dalilin da ya sanya a shekarar 2019 Jam’iyyar PDP ta tsayar dashi takarar kujerar Gwamnan jihar Kaduna inda suka fafata da gwamna mai ci El Rufa’i, masu nazarin al’amurran siyasa sun tabbatar da irin rawar ganin da ya taka a wannan za?e kuma jama’a sun shaida hakan duk da murdiya da magu?un da Jam’iyya mai mulki ta yi a lokacin.
Sirrin nasarorin Alhaji Isa Ashiru Kudan a fili suke duba da yadda ya rungumi kowa ba tare da nuna son kai ko wariya ta addini da kabila ba, tabbas irin wannan shugaba ake da bukata wanda zai daidaita komai.
Hakika jama’ar Jihar Kaduna wannan wata dama ce da Allah ya baku, inda mai girma Sarkin Bai Alhaji Isa Ashiru Kudan ya kasance ya amince da fitowa domin neman kujerar Gwamnan jihar Kaduna a babban za?e dake tafe na 2023, nauyi ne a kanku ku fito ku za?i wannan bawan Allah domin ceto Jihar daga mawuyacin halin da take ciki.
??Aminu Ahmad Marubuci na musamman a kafafen sadarwa na zamani
