Buhari Ne Ya Bada Umarnin Tsige Mai Mala Buni – El Rufa’i

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya goyi bayan cire gwamnan Yobe Mai Mala Buni a matsayin shugaban riko na Jam’iyyar APC.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufai ya bayyana haja a hirar da kafar talabijin ta Channels ta yi da shi ranar Talata, dangane da danbarwar da ake ciki a shugabancin APC.

Malam Nasiru El Rufai ya ?ara da cewar gwamnan jihar Neja Sani Bello ya samu goyon bayan Buhari da kuma gwamnonin APC 19.

Sannan ya ce Buhari ne ya ce a cire gwamnan Yobe Mai Mala Buni kai tsaye ba tare da ?ata lokaci ba.

“Buhari ne ya bayar da umarnin a cire shi kuma aka aiwatar, yanzu gwamna Bello ne ya gaje shi,” kamar yadda El Rufai ya bayyana.

Ya ce Mai Mala Buni wanda ba ya ?asar zai dawo ne a matsayin gwamnan Yobe amma ba matsayin shugaban jam’iyyar APC ba.

Related posts

Leave a Comment