Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar samar da lambar ?an kasa, NIMC, ranar Alhamis, ta sanar da cewa yan Najeriya sama da miliyan 60m sun yi rijistar lambar NIN, domin dacewa da umarnin ma’aikatar Sadarwa ?arkashin jagorancin Minista Pantami.
An ruwaito cewa ya zuwa yanzun NIMC na da bayanan wannan adadin na yan Najeriya a ?unshin ajiye bayananta (NIDB). Hukumar ta kara da cewa an samu wannan nasarar ne da ha?in kan masu ruwa da tsaki a ?angaren, wanda ya ha?a da gaba ?aya yan Najeriya.
Mr. Kayode Adegoke, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Alhamis. “Hukumar NIMC na farin cikin sanar da cewa sama da yan Najeriya miliyan 60m sun yi rijistar lambar zama ?an kasa NIN.” “A hukumance, mun gama duk wani shiri na rike wannan nasarar ta gudanar da rijistar katin zama ?an ?asa NIN a fa?in ?asa baki daya.”
“Hakan zai bada damar samun sahihan bayanan gane kowa, tantance kowa da kowa, da kuma ayyuka su rinka kaiwa ga kowane ?an Najeriya.”
Adegoke ya yaba wa ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Pantami, bisa kyakkyawan jagorancinsa wajen samun nasarar wannan aikin. Ya ?ara jaddada cewa lambar NIN ita ce babbar hanyar da za’a samu bayanai da gane kowane ?an Najeriya da kuma wanda doka ta ba shi damar zama a cikin ?asa.
